Home Labaru Kiwon Lafiya Gobara Ta Lashe Rumfuna Shida A Kasuwar Jihar Kebbi

Gobara Ta Lashe Rumfuna Shida A Kasuwar Jihar Kebbi

378
0

Rahotannin daga jihar Kebbi, sun tabbatar da cewa gobara ta lashe rumfuna shida a yayin da tashi a daren Juma’a a babbar kasuwar Birnin Kebbi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wutar ta tashi ne a jerin shagunan siyar da magungunan da ake amfani da su a gonaki da kuma sauran kayayyakin gona da ake siyarwa a kasuwar.
Wani mai kula da kasuwar, Aminu Shehu, ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu ba su tantance musabbabin tashin gobarar ba.
Shehu ya tabbatar da cewa gudummawar da jami’an kashe gobara suka kawo, shi ya kawo karshen gobarar har ya zama ba ta tsallaka zuwa wani bangare ba.
Bayanai sun tabbatar da cewa an yi asarar miliyoyin sakamakon wannan gobarar da ta tashi.

Leave a Reply