Mutane da dama ne ake fargabar an rasa su a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun, a yankin Wukari na Jihar Taraba.
Wasu ganau da suka gujewa rikicin a kudancin jihar sun tabbatar da kone tarin gidaje baya ga farwa juna tsakanin kabilun biyu masu rikici da juna.
Rahotanni sun ce yanzu haka rikicin ya haddasa gagarumar asara a kauyukan kabilun biyu ciki har da Wukari, da Kwatan Sule, da Chonku, da kuma iyakokin garuruwan Jootar da Vaase.
Shugaban kabilar Jukun Bako Benjamin, ya shaidawa manema labarai cewa duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma da kabilar ta Tibi a makon jiya, har yanzu suna ci gaba da kawo musu farmaki.
A cewar sa da sanyin safiyar Asabar dinnan ne, ‘yan kabilar ta Tibi suka sake farmakar, kauyukan su tare da kone gidaje baya ga kisan wasu mutane 15 matakin da ya sanya matasan kabilar ta Jukun mayar da martini.
Rahotanni sun ce ko a ranar alhamis ma makamancin rikicin ya hallaka mutane 12.
Tuni dai Rundunar ‘yan sanda jihar ta Taraba ta tabbatar da afkuwar rikicin inda ta ce jami’an na kokarin kwantar da hankula.
You must log in to post a comment.