Home Labaru Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Nazarin Cire Tallafin Mai –Ministar

Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Nazarin Cire Tallafin Mai –Ministar

369
0

Ministar kudi Zainab Ahmad, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara nazarin hanyoyin da za ta bi wajen ganin ta daina biyan kudaden tallafin man fetur, domin samun karin kudin shiga ga gwamnati.
Ministar ta shaida hakan ne bayan taron da asusun bada lamuni na duniya da hadin gwiwar bankin duniya, suka gudanar a birnin Washington na kasar Amurka.
Ta ce wannan ya biyo bayan shawarar da asusun bada lamunin ya ba Nijeriya da sauran kasashen duniya ne kan Tallafin man fetur.
Asusun bada lamunin ya bayyana cewa cire tallafin zai kara taimakawa gwamnati ta samu kudin shiga, sannan za a kara samun kudaden da za a gudanar wa ‘yan kasa ayyukan more rayuwa irin su hanya mai kyau, da asibiti da sauran ababen more rayuwa.
Ta ce wannan shawara ce mai kyau, amma dole a yi nazarin yadda za a aiwatar da ita, ta hanyar da ba za ta samu nakasu ba, sannan a samu nasara mai daurewa wajen aiwatarwar sannan kana a wayar da kan ‘yan kasa ma’anar cire tallafin.
Ta kara da cewa, akwai jan aiki a gaba, domin dole a wayar wa al’ummar Nijeriya kai kan wannan batun na cire tallafin, kuma za a yi a hakan ne a tsanake, don haka dole a ba da lokaci

Leave a Reply