Jam’iyyar APC ta shaida wa Kotun Sauraren Kararrakin zabe cewa, dan takarar shugabann kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba dan Nijeriya ba ne.
Jam’iyyar APC ta ce, Atiku Abubakar dan kasar Kamaru ne, don haka bai cancanci tsayawa takarar shugabancin Nijeriya ba.
APC ta kuma roki kotu ta soke takarar Atiku, ta kuma bayyana cewa dukkan kuri’un da ya samu sama da milyan 11 haramtattu ne.
Babban lauyan da ke jagorantar lauyoyin APC Lateef Fagbemi, ya ce an haifi Atiku Abubakar a ranar 26 Ga Nuwamba na shekara ta 1946 a garin Jada na jihar Adamawa, a lokacin ya na karkashin ikon kasar Kamaru kafin Turawan mulki su hade ta da Nijeriya.
Jam’iyyar APC, ta ce Atiku ba ya da hurumin kalubalanta ko tababar ilmin sakandaren shugaba Buhari, saboda lokacin da ya kamata kotu ta saurari batun takardun karatun shugaba Buhari ya wuce, kuma ba hurumin kotun sauraren kararrakin zabe ba ne ta saurari irin wannan bahasi.