Home Labaru Ana Daf Da Kawo Ƙarshen Tu’Ammili Da Miyagun Ƙwayoyi A Nijeriya –...

Ana Daf Da Kawo Ƙarshen Tu’Ammili Da Miyagun Ƙwayoyi A Nijeriya – Marwa

11
0

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi Buba Marwa, ya ce ana daf da kawo karshen matsalolin safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.

Buba Marwa ya shaida wa manema labarai cewa, da tallafin gwamnati da manyan masu ruwa da tsaki Nijeriya za ta yi nasara a kan fataucin miyagun ƙwayoyi.

Marwa, ya bayyana matsalar miyagun ƙwayoyi a matsayin wata annoba a Nijeriya, sai dai ya ce hukumar sa na yin dukkan mai yiwuwa domin ganin an magance matsalar, kuma su na samun goyon bayan da ya dace daga gwamnatin tarayya.

Buba Marwa ya kara da cewa, hukumar NDLEA ta na shirin shiga ƙananan hukumomi domin wayar da kan mutane.