Home Labaru Zagayowar Ranar Maulidi: Sanata Ahmad Lawan Ya Taya Musulmin Najeriya Murna

Zagayowar Ranar Maulidi: Sanata Ahmad Lawan Ya Taya Musulmin Najeriya Murna

15
0

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar Maulidi a wata sanarwa da ya fitar.

Ahmad Lawan ya ce ranar Maulidi rana ce da ya kamata
Musulmi da sauran mabiya wasu addinan su tuna da alfanun
zaman lafiya da girmama juna da tsoron Allah kamar yadda
Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi Wasallam ya koya mana
tsawon rayuwar sa.

Ya ce yin hakan na da matukar amfani a yanzu da ake tsananin
bukatar waɗannan halaye na sa don kawo waraka a ƙasar mu
tare da karfafa danƙon zumunci a matsayin mu na mutane masu
imani kuma ƴan Najeriya.

Shugaban majalisar dattawan ya ce gwamnatin Najeriya da
Majalisar dokoki za su ci gaba da yin aiki sosai don samar da
yanayi mai kyau na zaman lafiya da fahimtar juna da ci gaba
Najeriya.

Ya kuma bukaci ,yan Najeriya su ci gaba da addu’a da tallafa wa
hukumomin tsaro a koƙarin su na kare lafiya da dukiyoyin
al’umma.