Home Labaru An Samu Kwamacala A Zaben APC Na Jihar Akwa Ibom

An Samu Kwamacala A Zaben APC Na Jihar Akwa Ibom

16
0

An samu hargitsi a jam’iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom bayan zaben shugabannin jiha da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, bayan mutane hudu kowanen su ya yi ikirarin shi ne shugaban jam’iyyar na jihar.

Wata majiya ta ce, Augustine Ekanem da Steve Ntukekpo da Douglass Pepple da wani mutum ne kowa ke da’awar cewa APC ta na hannun su, yayin da na karshen su ke tare ne da bangaren wani fitaccen jigon APC a jihar Akwa Ibom Bishop Akpan.

Steve Ntukekpo dai ya zama shugaban jam’iyyar ne bayan ya samu wasu na kusa da Ministan Neja-Delta Godswill Akpabio sun zabe shi a zaben da su ka shirya.

Bangaren Sanata Ita Enang kuma sun gudanar da na su zaben shugabannin, inda su ka tsaida Douglass Pepple a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Sai dai Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya Dr. Ita Udose, ya bayyana Augustine Ekanem a matsayin sahahin shugaban jam’iyyar APC da ya lashe zaben.