NAHCON na ci gaba da jigilar maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali a bana.
Ta wallafa a shafinta na X, zuwa yau Asabar da safe jirage 12 ne ɗauke da maniyyatan suka isa Saudiyya.
Hukumar ta ce 11 daga cikin jiragen sun sauka ne a birnin Madina, yayin da ɗaya kuma ya sauka a Jedda.
NAHCON ta ce daga cikin adadin Da suka isa ƙasa mai tsarkin 2934 maza ne, yayin da 2140 mata ne.
A makon nan NAHCON ta fara jigilar maniyyatan, inda aka fara da jihohin Kebbi,Bauchi,Nasarawa,Legos da Abuja.














































