Home Labaru Adadin Wadanda Su Ka Mutu A Ginin Legas Ya Kai Mutane 44

Adadin Wadanda Su Ka Mutu A Ginin Legas Ya Kai Mutane 44

86
0

Adadin wadanda su ka mutu a ruftawar dogon ginin anguwar Ikoyi da ke Legas ya kai 44, kwanaki bakwai bayan ginin mai hawa 21 ya ruguje, inda har yanzu ake kan neman wasu da dama da lamarin ya rutsa da su.

Daga cikin wadanda aka zakulo gawarwakin su akwai mamallakin ginin Femi Osibona, da abokin sa Wale Bob-Oseni da kuma mai taimaka ma shi Oyinye Enekwe da dai sauran ma’aikatan sa.

A ranar Asabar da ta gabata ne, hukumomi su ka ba al’umma damar binciken gawawwakin da aka jibge a dakin ajiyar gawa da ke asibitin Mainland a Lagos domin gano ‘yan’uwan su.

Tuni dai gwamnatin jihar Lagos ta dakatar da shugaban hukumar kula da gine-ginen jihar daga aiki.