Home Labaru Hukumar NAHCON Ta Rufe Karbar Kudin Kujera

Hukumar NAHCON Ta Rufe Karbar Kudin Kujera

227
0
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON

Hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON, ta ce za ta rufe karbar kudin kujerar aikin hajjin bana daga ranar Litinin 15 ga watan Yuli matukar tsarin bai sauya ba.

Wannan kuwa ya biyo bayan kara wa’adin lokacin biyan kudin ne, bayan samun wani ragi a farashin kujerar da fiye da Naira dubu 50.

Karanta Labaru Masu Alaka: Alhazan Nijeriya 2139 Sun Isa Kasa Mai Tsarki – NAHCON

Shugaban hukumar Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed, ya ce za a kammala amsar kudin don sama wa dukkan maniyyatan izinin tafiya gudanar da aikin hajjin.

Tun ranar Larabar da ta gabata ne, aka kaddamar da fara jigilar alhazai daga jihar Katsina, inda wasu yankuna kamar Kaduna rukunin alhazan su ka sauka a Saudiyya.