Home Labaru An Sake Dage Shari’ar Sheikh Abduljabbar Zuwa Watan Gobe

An Sake Dage Shari’ar Sheikh Abduljabbar Zuwa Watan Gobe

10
0

A Ranar Alhamis din nan aka ci gaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar kan Abduljabbar Nasiru Kabara, inda take zarginsa yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Masu shigar da karar sun gabatar da shaidu mutum 12 inda Lauyoyi masu shigar da kara karkashin jagorancin Barista Siraj Sa’id (SAN) suka bayyana gaban Mai shari’a Ibrahim Sarki, a kotun shari’ar Musulunci dake birnin Kano.

Shaidun masu kara su 12 sun gabatar da shaida inda masu kare Abduljabbar suka nemi kotu ta bashi izinin bada shaida da kansa, kuma nan take kotun ta amince da bukatar lauyoyin.

Mai shari’a Sarki Yola ya bayyana cewa: Sai dai Abduljabbar ya kare kanshi daga farkon Shari’ar har karshenta, sai ya sallami lauyoyinsa; ko kuma ya yi shiru lauyoyinsa su ci gaba da kare shi har karshen Shari’ar.

A nasa bangaren Abduljabbar yace Shari’ar da ake yi masa ta hadisai ce, saboda haka ba wani lauya da zai iya tsaya mishi.

To sai dai bayan tafka muhawara an sake dage shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, domin ci gaba da muhawara kan batun ko lauyoyi zasu kare Abduljabbar din, ko shine zai kare kansa.