Home Labaru Iyaye Sun Roki Gwamnati Ta Bude Makarantu A Jihar Zamfara

Iyaye Sun Roki Gwamnati Ta Bude Makarantu A Jihar Zamfara

78
0

Wasu iyayen yara a jihar Zamfara, sun koka a kan rashin buɗe makarantu, inda su ka ce rashin komawa makarantun alama ce da ke nuna cewa dubban ‘ya’yan talakawa za su cigaba da zaman gida tsawon zangon karatu na biyu ke nan.

Gwamnatin jihar Zamfara dai ta rufe makarantun jihar ne a farkon watan Satumba, bayan sace gomman ɗalibai daga Sakandaren Ƙaya da ke ƙaramar hukumar Muradun.

Wani uba ya shaida wa manema labarai cewa su na tsaka mai wuya, sannan ya yi kira ga gwamnatin jihar ta dubi girman Allah ta bude masu makarantu.

Iyayen yara a jihar Zamfara, sun ce tuni ‘ya’yan su sun fara manta karatu.