Home Labaru INEC Ta Bayyana Dr Bello Mutawalle Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

INEC Ta Bayyana Dr Bello Mutawalle Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

511
0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya watau INEC ta bayyana Dr. Bello Mutawalle, na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe gwamnan Jihar Zamfara.

Inec ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon watsi da ‘yan takarar Jam’iyyar APC da kotun koli tayi, saboda abinda ta kira rashin gudanar da zaben fidda gwani a matakai daban daban.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana Mutawallen, a matsayin zababben gwamnan saboda shi ya zo na biyu a yawan kuri’un da aka kada a zaben da akayi a watan Maris.

Farfesa Mahmud Yakubu yace Mutawalle ya cika duk sharuddan da ake bukata, saboda haka shine zababben gwamna da za’a ba takardar shaidar lashe a ranar litinin idan Allah ya kaimu.

Leave a Reply