Home Home Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar PDP Reshen Kano

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar PDP Reshen Kano

26
0
Wutar rikici ta ƙara ruruwa a jam’iyyar PDP ta jihar Kano, duk kuwa da hukuncin kotu na baya-bayan nan da matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya banagaren jam’iyyar.

Wutar rikici ta ƙara ruruwa a jam’iyyar PDP ta jihar Kano, duk kuwa da hukuncin kotu na baya-bayan nan da matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya banagaren jam’iyyar.

Lamarin dai ya faru ne, bayan ɓangen Sadiq Wali da wata kotun tarayya ta ce ba shi ne ɗan takarar gwamnan ba, amma ya ɗaukaka ƙara daga baya ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen sa a jihar Kano.

Sai dai ɓangaren da kotu ta ce Muhammad Abacha ne halastaccen dan takara ya yi Alla-wadai da wannan mataki, ya na cewa nuna raini ne ga kotu.

Bayanai sun nuna cewa, a wannan makon ne ake sa ran kwamitin yaƙin neman zaben da ɓangaren Sadiq Wali ya ƙaddamar zai fara zama domin tattauna yadda zai gudanar da aikin sa.

Sai dai Ɓangaren Muhammad Abacha sun ce ba su tare da wannan mataki, yadda lauyan jam’iyyar PDP a Kano Barista Ibrahim Isa Wangida ya shaida wa manema labarai.