Rahotanni sun ce, an rufe ofishin jakandancin Nijeriya da ke London a Burtaniya, bayan wasu jami’an diflomasiyya biyu sun kamu da cutar COVID-19.
A cikin wata sanarwa da hukumomin ofishin jakadancin suka fitar ta ce, Ofishin zai cigaba da kasancewa a rufe har na tsawon kwanaki goma kamar yadda dokar yaki da cutar ta tanada a Burtaniya.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaban ofishin kula da shige da fice da wasu jami’ai biyu, sun halarci wani taro wanda bayan dawowarsu ne aka gudanar da gwajin jami’an.
Sanarwar ta cigaba da cewa, a bisa ka’idojin yaki da cutar COVID-19 da kuma bukatar ganin an bi sharuddan kasar, ofishin zai kasance a rufe na tsawon kwanaki 10 domin bin dokar killace wadanda suka yi mu’amulla da jami’an.
You must log in to post a comment.