Hedkwatar tsaro ta Nijeriya, ta ce dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga 123 a jihar Zamfara.
Jami’an rundunar sun tarwatsa mabuyar ‘yan bindigar a dajin Dansadau da Kuyambana da Sabubu da kuma yankin Dudufi.
Mai magana da yawun hedikwatar tsaron, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce an samu wannan nasara ne a cikin makonni biyu da suka gabata.
Ya ce, dakarun rundunar Operation Whirl Stroke da ke jihar Taraba sun kama ‘yan bindiga da masu taimaka masu da bayanan sirri a jihohin Benue da Taraba.
Onyeuko ya kara da cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda shida, da bindigar SMG guda da kananan bindigogi biyu, da jigidar harsashin NATO guda 66 mai tsawon mita 7.62 a hannun miyagun.
A cewarsa, jami’an tsaron sun kashe ‘yan ta’adda 27, yayinda suka kama wasu 51, sannan wasu sama da dubu 1 sun mika kansu.