Home Labaru Kiwon Lafiya Wata Sabuwar Cuta Mai Kama Da Ebola Ta Bulla A Kasar Guinea,...

Wata Sabuwar Cuta Mai Kama Da Ebola Ta Bulla A Kasar Guinea, Kusa Da Najeriya

54
0
Wata Sabuwar Cuta mai Kama Da Ebola Ta Bulla A Kasar Guinea, Kusa Da Najeriya

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce wata sabuwar cuta da ake kira Marburg ta bulla a kasar Guinea.

Wannan dai shi ne karo na farko da wata cuta mai kama da Ebola ta bulla a yankin yammacin Afrika.

Wata majiya ta ce, an dauki samfurin cutar ne daga jikin wani mara lafiya a Gueckedou, inda aka tabbatar da cutar Marburg, a yankin ne aka samu cutar Ebola a 2021 da kuma shekara ta 2014 zuwa 2016.

Bullar cutar dai na zuwa ne watanni biyu bayan kasar Guinea ta sanar da bacewar cutar Ebola.

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga cikin jemagu kuma tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum ta zufar jiki ko idan yawun mutum ya fada kan abubuwa.

Kawo yanzu dai, babu rigakafin cutar kuma babu maganinta, sai magungunan da ake rage radadi.

An fara gano cutar Marburg ne a shekara ta 1967, inda mutane 31 suka yi rashin lafiya a Jamus da Yugoslavia inda aka gano cutar a jikin birrai a kasar Uganda.