Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta tsaida ranar 7 ga watan Satumba domin sauraren karar da ke neman a haramta wa Bola Tinubu takara a zaben shekara ta 2023.
Masu shigar da karar, wadanda jiga-jigan jam’iyyar APC ne guda hudu, sun nemi kotu ta yanke hukuncin cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 ba, saboda zargin ya mika takardun karatu na bogi ga hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC.
An dai zargi Bola Tinubu da gabatar da takardun karatu na bogi, lamarin da ya janyo cece-kuce da tarin muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Haka kuma, an zargi Bola Ahmed Tinubu da aikata laifuffukan da su ka shafi harkokin safarar miyagun kwayoyi da badakalar gidaje a kasar Amurka, sai dai Tinubu ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.














































