Home Labaru Ba Za Mu Sa Dokar Ta Baci Ba A Najeriya – Ministan...

Ba Za Mu Sa Dokar Ta Baci Ba A Najeriya – Ministan ‘Yan Sanda

70
0

Ministan Lamurran ‘yan sanda na Najeriya Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce babu buƙatar sanya dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro a Najeriya.

Minista Dingyadi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis, inda yake amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa gwamnati ta yanke hukuncin yi wa ƴan sanda ƙarin albashi.

Ya ce duk da cewa Najeriya ƙasar dimokradiyya ce kuma kowa na da damar faɗin albarkacin bakin sa, amma dai ba a yi shirin sanya dokar ta ɓaci a kan waɗannan matsaloli ba.

Ƴan Najeriya dai sun daɗe suna kiraye-kirayen a sanya dokar ta ɓaci a jihohi musamman na yankin arewa maso yamma, duba da halin taɓarɓarewar tsaro da yankin ke ciki na hare-haren ƴan bindiga da satar mutane.