Home Home ‘Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa Na Naira Miliyan 250 A Wajen...

‘Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa Na Naira Miliyan 250 A Wajen Wasu ‘Yan Katsina

47
0
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa su na cikin firgici, bayan ‘yan ta’addan da su ka sace mazauna kauyen 43 sun bukaci a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa kafin sako mutanen da su ka yi garkuwa da su.

Majiyoyi da dama sun ce, ‘yan ta’addan sun kai wa kauyen Bakiyawa hari ne, inda su ka kashe mazauna garin hudu tare da yin garkuwa da wasu 44, bayan sun tafka sata a shaguna tare da kore shanu da dama.

Rahotani sun ce, ana cikin halin rashin tabbas game da makomar wadanda ‘yan bindigar su ka sace, duba da cewa babu alamun hada makudan kudaden da ake nema  a matsayin fansa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce babu wani bayanin da ya samu a hukumnce game da kudin fansar da ‘yan bindigar su ke nema.