Home Labaru An Kama Mutane 4 Bisa Zargin Ƙona Gonar Obasanjo Da Gangan A...

An Kama Mutane 4 Bisa Zargin Ƙona Gonar Obasanjo Da Gangan A Benue

119
0

Rahotanni na cewa, yanzu haka an kama mutane hudu bisa zargin su da cinna wuta a gonar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Jihar Benue.

Gonar Obasanjo dai ta na yankin Howe ne da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benue, a wani katafaren filin da ake noman mangwaro da wasu kayayyakin abinci masu yawa.

An dai kama mutanen ne kwanaki kadan bayan cinna wuta a gonar mai girman hecta dubu 2 da 420, lamarin da mai magana da yawun Obasanjo Kehinde Akinyemi ya bayyana a matsayin abin takaici.

Bayan afkuwar lamarin, mahukunta a Jihar ciki har da gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, sun sha alwashin binciko wadanda su ka tafka barnar domin a hukunta su.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya ce an gano cewa da gangan aka cinna wa gonar wuta, don haka dole a hukunta wadanda su ka aikata laifin.