Home Labaru Boko Haram Sun Janyo Asarar Dala Biliyan 6.9 – Zulum

Boko Haram Sun Janyo Asarar Dala Biliyan 6.9 – Zulum

68
0

Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum, ya ce aƙalla an yi asarar dala biliyan 6 da miliyan 900 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya a cikin shekaru 13.

Zulum ya bayyana haka ne, yayin zantawa da manema labarai a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya shaida masu cewa hare-haren ta’addanci sun haifar da ƙuncin talauci da shiga ƙangin mummunar rayuwa da sauran manya da ƙananan matsalolin da al’ummar yankin su ka shiga.

Ya ce Boko Haram sun haddasa mummunan bala’in gudun hijira tare da lalata gidaje da ƙauyuka da garuruwa, baya ga asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi da haddasa fatara da talauci da kuma illata tattalin arzikin yankin.

Zulum ya cigaba da cewa, duk da haka sakamakon ƙoƙarin dawo da zaman lafiya na Bankin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya su ka yi, ya nuna cewa aƙalla yankin Arewa maso Gabas ya yi asarar dala biliyan 6 da miliyan 900, kuma jihar Borno ke da kashi 2 bisa 3 na asarar da aka tafka gaba ɗaya.