Home Labaru An Tsinci Gawar Mai Gadi Da Iyalan Sa Uku A Wani Gidan...

An Tsinci Gawar Mai Gadi Da Iyalan Sa Uku A Wani Gidan Gona A Abuja

69
0

Rahotanni daga birnin Abuja na cewa, an tsinci gawarwakin wasu iyalai hudu a wani gidan gona da ke yankin karamar hukumar Abaji.

Wata majiya ta ce, an samu gawarakin mai gadin gidan gonar Dominic Peter Adegeze da yaran shi mata biyu da kuma dan sa mai wata daya a duniya kwance, yayin da aka kwashi matar sa Laraba a sume zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja da ke  Gwagwalada.

Wani ma’aikacin gidan gonar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce lamarin ya afku ne a ranar Alhamis da ta gabata, ya na mai cewa wani ma’aikaci ya je ba wasu dabobbi abinci a gonar sai ya tarar da ainihin kofar mashigin rufe da makulli, don haka ya haura katanga sannan ya ga mai gadin da iyalin sa su na nishi da kyar kuma kumfa ya na fita ta bakunan su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya DSP Adeh Josephine ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.