Jami’an ‘Yan sanda a Legas, sun ce sun kama mutane 12 bisa zargin su da hannu a kisan wani jami’in rundunar mai suna Kazeem Abonde.
Kazeem Abonde, wanda lauya ne kuma mai muƙamin sufiritanda, an kashe shi ne bayan watanni shida da yin ritaya, yayin wani samame da aka kai mafakar waɗanda ake zargi da aikata laifuffuka a rukunin gidaje na Ajao.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Legas Adekunle Ajisebutu ya fitar, ya ce za a gurfanar da waɗanda aka kama gaban kotu.
Kakakin ‘yan sandan, ya ce daga cikin wadanda aka kama har da wani mai suna Isma’il Abdullahi Haruna mai shekara 23, yayin da aka kama sauran mutane 11 bayan makonni huɗu ana gudanar da bincike.
You must log in to post a comment.