Home Labaru Kasuwanci N2Tr Cbn Ya Rarraba Wa Masu Kananan Sana’O’I Da Kamfanoni – Emefiele

N2Tr Cbn Ya Rarraba Wa Masu Kananan Sana’O’I Da Kamfanoni – Emefiele

14
0

Gwamnan Babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya ce an raba tsakanin naira tiriliyan biyu zuwa uku ga masu kanana da matsakaita da manyan masana’antu daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu, domin a ba su damar farfadowa da ga illar annobar korona.

Emefiele ya bayyana haka ne, a wata tattaunawa da aka yi da shi a kasuwar duniya ta kasashen Afrika a Durban na kasar Afrika ta kudu.

Ya ce Nijeriya ta fuskanci illar annobar a shekarar da ta gabata, lamarin da ya sa shugaba Buhari ya kira shi tare da ministar kudi, inda ya umarce su da a fitar da tsarin tallafin rage radadin annobar korona.

Gwamnan babban bankin, ya ce tallafin, wanda daga baya aka kara yawan wadanda aka ba, bashi ne ba kyauta ba kamar yadda wasu ke zato.

Emefiel ya tabbatar da cewa, a sauran shekarun da su ka rage wa mulkin Buhari da kuma wa’adin sa, za su maida hankali wajen samar da ababen more rayuwa da samar da ayyuka, domin  habaka tattalin arziki tare da shawo kan matsalar tsaro.