Home Labaru Ilimi An Kaddamar Da Shirin Boko Halal Domin Daƙile Tsatsauran Akidu A Borno

An Kaddamar Da Shirin Boko Halal Domin Daƙile Tsatsauran Akidu A Borno

14
0

Wata gidauniya mai zaman kan ta a birnin Maiduguri na jihar Borno, ta kaddamar da wani littafi mai suna Boko Halal domin daƙile al’adar kaifin kishin Islama.

Littafin na Boko Halal dai, da an fara rubuta shi ne da yaren Ingilishi, kafin daga bisani aka fassara zuwa harsunan Hausa da Kanuri.

Shugabar gidauniyar Hamsatu Allamin, ta ce bijiro da wannan manufar yayin da ake cika shekaru 12 da rikicin Boko Haram, za ta koyar da mutane ainihin sakonnin addinin musulunci.

A shekara ta 2016 ne aka soma bijiro da littafin Boko Halal, kafin sauran kungiyoyi su sake nazartar shi da shawarwarin su, wadda aka rubuta da zummar jan hankali yara masu tasowa tare da cusa masu dabi’u masu alfannu ga ci-gaba al’umma.