Home Labaru Gwamnatin Jigawa Ta Yi Asarar Naira Miliyan 100 Sanadiyar Sace-Sace

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Asarar Naira Miliyan 100 Sanadiyar Sace-Sace

12
0

Gwamnatin Jihar Jigawa, ta ce ta yi asarar Naira miliyan 100 sanadiyar sace-sacen injinan fanfon tuka-tuka a shekara ta 2020.

Kwamishinan Ruwa na jihar Jigawa Ibrahim Garba Hannun-Giwa, ya ce a shekara ta 2020 an sace fanfunan tuka-tuka sama da 163, lamarin da ya ce ya na janyo cikas wajen samar da ruwan sha ga al’ummar Jihar.

Garba Hannun Giwa,  ya ce ɓarayin su kan ɗauki tsawon sa’o’I suna tu ge injinan famfunan tuka-tuka, duk kuwa da kasancewar mutanen gari su na kallo ba a iya kama su ko gane ko su wanene ba.

Ya ce gwannati ba za ta kasance a ko’ina ba, don haka ya zama dole jama’ar gari su rika sa ido a kan injinan domin kare su daga fataken dare.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwannatin jihar ta kashe Naira Biliyan 22 a cikin shekaru shida wajen samar da ruwan sha ga al’ummar jihar Jigawa.