Home Labaru An Gano Yadda Mayaƙan Boko Haram Ke Haɗa Kai Da ‘Yan Bindiga

An Gano Yadda Mayaƙan Boko Haram Ke Haɗa Kai Da ‘Yan Bindiga

21
0

Wasu shugabannin Amurka sun gano yadda mayaƙan Boko Haram da ke Arewa maso gabashin Nijeriya ke haɗa kai da ‘Yan bindigar da ke kai hare-hare a arewa maso yamma.

Jaridar Wall Street Journal ta ƙasar Amurka ta ruwaito cewa, Amurka ba ta ganin ‘yan bindiga a matsayin barazana a gare ta, amma jami’ai sun dade su na sa ido cewa akwai yiwuwar alaƙar su da mayaƙan Boko haram.

Wani rahoto da jaridar ta wallafa, ya ce jami’an gwamnatin Amurka sun yi kutse a kan wani kiran waya daga wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, kuma an ji su na ba ‘yan bindiga shawara a kan garkuwa da mutane da tattaunawa domin karbar kuɗin fansa.

Rahoton, ya kuma jaddada kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari, ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, duk da cewa ba su da wani buri na siyasa ko addini.