Shugaban kamfanin sadarwa na Daar Communications Raymond Dokpesi ya riga mu gidan gsakiya.
Rahotanni sun ambato iyalan mamacin su na bada sanarwar mutuwar sa, amma ba su bayyana abin da ya yi sanadiyyar ajalin sa ba.
Gidan talabijin na AIT dai ya na ƙarƙashin kamfanin Daar Communications, wanda kuma ya mallaki gidan rediyo na Ray-Power.
Baya ga harkokin sadarwa, Raymond Dokpesi ɗan siyasa ne, wanda ya taɓa neman takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam’iyyar PDP.














































