Home Labaru An Fara Ce-Ce-Ku-Ce A Kan Sabanin Aisha Buhari Da Garba Shehu

An Fara Ce-Ce-Ku-Ce A Kan Sabanin Aisha Buhari Da Garba Shehu

441
0

Wasu ‘yan Nijeriya sun fara maidawa uwargidan shugaban kasa  Aisha Buhari martani a kalaman da ta yi na zargin mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu da rashin girmama ofishin ta bisa umarnin Mamman Daura.

Idan dai ba a manata ba, Aisha Buhari ta fitar da wata sanarwa da ke cewa Mamman Daura ya hada kai da Malam Garba Shehu domin yin watsi da matsayin ta na uwargidan shugaban kasa.

Wasu dai na zargin Aisha Buhari da kokarin dauke hankalin ‘yan Nijeriya a kan abubuwan da ke faruwa a kasa, yayin da wasu ke maida mata martani da cewa matsalar su ta cikin gida.

Aisha Buhari ta ce maimakon Garba Shehu ya maida hankali a kan aikin da shugaban kasa ya sa shi, sai ga shi ya wajen biyayya ga wasu ‘yan tsiraru a fadar shugaban kasa, sannan kuma ta zargi  shi da kullawa iyalan ta sharri da kuma yi wa ‘ya’yan ta sharri iri-iri.

Sannan Aisha Buhari ta kara da cewa, Garba Shehu ya yi kullalliya domin ganin an sallami hadiman ta kafin ta farga a dakile batun.

A karshe ta jan hankalin Garba Shehu da cewa aikin da ke gabanshi shine kare mutuncin shugaban kasa da kuma tallata irin ayyukan kwarai da gwamnatin ke aiwatarwa ba wai shiga sharo ba sahu ba.