Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umurnin tsare mabiya akidar Shi’a 60 a gidan gyara halin na kuje Abuja da na Suleja da ke jihar Neja.
Sai dai a lokacin zaman kotun na ranar talatar da ta gabata, lauyan ‘yan shi’an Bala Dakum ya bukaci a kotu da ta bada belin mutanan, matakin da kotun ta janyo hanlin sa da cewa takardan beli daya ya rubuta na bukatar belin mutanan 60, maimakon takardu 60.
Sannan mai shari’a Suleiman Belgore ya yi watsi da bukatar lauyan, lamarin da ya sa lauyan gwamnati Simon Lough ya bukaci kotu ta bada umurnin tsare ‘yan shi’an a kurkuku.
Idan
dai ba a manta ba, Jami’an ‘yan sanda sun kama ‘yan Shi’an 60 a ranar 22 ga
Yuli, jim kadan bayan sun gudanar zanga-zanga wacce ta yi sanadiyar mutuwar
babban jami’in dan sanda DCP Usman Umar, da kuma wani mai yi wa kasa hidima Precious
Owolabi a Abuja.