Home Labaru Kwaskwarima: Wasu Sanatoci Sun Bukaci A Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

Kwaskwarima: Wasu Sanatoci Sun Bukaci A Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

312
0

Majalisar dattawa ta yi watsi da bukatar wasu ‘yan majalisa na ganin tsige shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan daga mukamin sa.

‘Yan majalisar dai sun bukaci a kada kuri’un amincewa da tsige sanata Lawan ne  a cikin wata takardar korafi da aka gabatar a zauran majalisar, wanda da ke dauke da sunayen Sanatoci 36.

Manufar kada kuri’ar dai ita ce, tabbatar da goyon baya ga shugaban majalisar, amma idan masu adawa da shi su ka samu rinjaye, to akwai yuwuwar an kama hanyar tsige shi daga mukamin sa.

Sai dai wasu sanatoci sun yi mamakin yadda sunan su ya shiga cikin jerin sunayen, inda wani sanata daga yankin Arewa maso gabas ya ce, bai san dalilin da ya sa ake bukatar ganin yi wa shugabancin majalisa kwaskwarima ba.