Home Labaru An Fara Bitar Ayyukan Ministoci Na Tsakiyar Wa’Adin Mulki Na Biyu

An Fara Bitar Ayyukan Ministoci Na Tsakiyar Wa’Adin Mulki Na Biyu

169
0
Buhari

Gwamnatin tarayya, ta fara gudanar da taron bitar ayyukan ministoci na tsakiyar wa’adin mulki na biyu a birnin Abuja.

Shugaba Buhari ya yi jawabi yayin bude taron bitar, inda ya sake jadada cewa ya na kan bakan sa na tabbatar da cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zaben sa.

Daga cikin alkawuran da shugaba Buhari ya dauka dai akwai bunkasa tattalin arziki da yaki da ayyukan ta’adanci da samar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Wadanda ke halartar taron kuwa sun hada da mataimakin shugaba kasa Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da shugabannin majalisun tarayya Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila.

Yemi Osinbajo, ya ce tattalin arzikin Nijeriya ya na kan hanyar kara bunkasa daga zangon farkon shekara ta 2019, yayin da bullar annobar korona a zango na biyu na shekara ta 2021 ya janyo wa tattling arzikin cikas, inda aka samu durkushewar kashi 1 cikin 100.

Leave a Reply