Home Labaru Barazanar China: Taiwan Ta Sha Alwashin Kare Kan Ta

Barazanar China: Taiwan Ta Sha Alwashin Kare Kan Ta

216
0
CHAINA AND TAIWAN
Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ta mayar da martani kan jawabin Shugaba Xi Jinping na China, wanda a ranar Asabar ya yi gargadin cewa tsubirin mallakin kasar sa ne.

Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ta mayar da martani kan jawabin Shugaba Xi Jinping na China, wanda a ranar Asabar ya yi gargadin cewa tsubirin mallakin kasar sa ne.

Da take jawabi ta kafar talabijin na kasar a ranar tunawa da juyin juya halin Wuchang a shekarar 1911, tsai ta ce China ta daina mafarkin matsa wa al’ummar Taiwan lambar son mallakar kasar su ta kowacce fuska.

Ta kara da cewa Taiwan za ta ci gaba da bunkasa tsaron ta ta yadda babu wani da zai matsa mata yin biyayya ga China.

Taiwan na kallon kanta a matsayin ƙasa mai ‘yanci duk da matsin lambar da take fuskanta daga China na mallakar ta.

Leave a Reply