Hukumar cinikayya ta Amurka ta kakabawa shafin Facebook tarar dala biliyan biyar inda a yanzu ake jiran amincewar ma’aikatar shari’a domin kai karshen maganar.
Mamallakin shafin Facebook Mark Zuckerberg, bai ce komai ba kan wannan tarar da aka daurawa kamfanin sa.
Karanta labaru Masu Alaka: Kungiyar Eu Za Ta Lafta Wa Amurka Harajin Dala Biliyan 12
Wasu ‘yan adawa sun dade suna magana a kan a dauki mataki mai tsauri kan Facebook da kuma shugabansa Mark Zuckerberg, saboda yadda masu amfani da shi ke bankado wasu bayanan sirri.

Duk da cewar babu wani cikakken bayanin da aka fitar a kan lamarin, amma wasu na ganin cewa matakan da za’a dauka kan Facebook sun kasance masu tsauri.
Haka zalika wasu mutanen na da ra’ayin cewa shi kan shi mamallakin kamfanin Zuckerberg ya kamata a hukunta shi.
Shugabar cibiyar Dimokuradiyya da Fasaha, ta Amurka Nuala O’Connor, ta ce tarar na nuna muhimmancin da bayanan sirrin ke da shi ga masu amfani da shafin.
You must log in to post a comment.