Home Labaru Sojojin Nijeriya Na Samun Nasara A Yaki Da Ta’addanci – Buhari

Sojojin Nijeriya Na Samun Nasara A Yaki Da Ta’addanci – Buhari

267
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, jami’an tsaro na samun gagarumin nasara a yaki da ake yi da ta’addanci a Najeriya.

Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a bikin yaye manyan hafsoshi na kwas na 41 da aka yi a makarantar horar da manyan hafsoshin soji na Jaji dake Kaduna.

Karanta Labaru Masu Alaka: Shugaba Buhari Ya Yi Wa Wasu Hafsoshin Soji Karin Girma

Shugaban kasa Buhari, ya yaba da irin hadin kan da ake samu daga kasashen makwabta a yakin da ake tafkawa da yan ta’addan kungiyar Boko Haram, ya ce hakan ya raunana karfin yan ta’adda a yankin gaba daya.

Ya ce ‘yawancin matsalolin tsaron da ake fama da su a Najeriya suna da dangantaka da iyakokinmu domin haka ne aka kafa dakarun yankin Afrika kuma dole a ci gaba da samun hadin kai tsakanin sojojin kasashen gaba daya. ‘

Karanta Labaru Masu Alaka: Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kafa Kotun Hukunta Sojoji

Shugaban kasa ya bayyana ci gaba da goyon bayan gwamnatin tarayya wajen jin dadin hafsosi da dakarun rundunar tsaron Nijeriya ta hanyar horar da su da samar musu da kayayyakin aiki.