Home Labaru Wata Sabuwa: Jinkirin Nadin Ministoci Ya Jefa Ma’aikatu 3 Cikin Kunci

Wata Sabuwa: Jinkirin Nadin Ministoci Ya Jefa Ma’aikatu 3 Cikin Kunci

397
0

Sakamakon jinkirin nadin ministocin shugaba Muhammadu Buhari bayan kwanaki 45 da kafuwar sabuwar gwamnatin sa a wa’adi na biyu, wasu manyan ma’aikatun tarayya sun shiga halin ni-‘yasu na tsaikon harkokin gudanarwa.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya karbi rantsuwar wa’adin mulki na biyu tun a ranar 29, ga watan Mayu na shekara ta 2019, amma har yanzu ya na ci-gaba da jinkirin nadin ministocin sabuwar majalisar zartarwa ta kasa.

Yanzu haka dai ana cikin matsanaciyar bukatar kafuwar sabuwar majalisar zartarwa domin tunkarar kalubalen rashin tsaro da tattalin arziki da ke barazanar ingiza Nijeriya cikin kangi na koma baya.

Binciken wata majiyar manema labarai ya tabbatar da cewa, wasu manyan ma’aikatu gwamnatin tarayya uku sun tsaya cak, wajen ci-gaba da gudanar da ayyukan da su ka rataya a wuyan su, saboda rashin ministocin da za su rike akalar su ta jagoranci.

Manyan ma’aikatun uku kuwa sun hadar da ta lafiya, da tsaro da kuma ilimi.

Leave a Reply