Home Labaru Ba Za Mu Sake Yarda Da Juyin Mulki A Yammacin Afirka Ba...

Ba Za Mu Sake Yarda Da Juyin Mulki A Yammacin Afirka Ba – Shugaba Tinubu

250
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba za su sake yarda
da juyin mulki a kasashen Yammacin Afirka ba.

Tinubu ya bayyana haka ne, jim kadan bayan an zabe shi a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS, inda ya ce dole ne su jajirce kan mulkin Dimokuradiyya.

Ya ce babu gwamnati da ‘yanci da doka idan babu tsarin dimokuradiyya, don haka ba za su sake yarda da juyin mulki a Yammacin Afirka ba.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa, babu wani daga cikin su da bai yi yakin neman zabe domin ya zama shugaba ba, kuma ba su ba sojojin su kudi da zuba jari a kan su da horar da su don su take ‘yancin jama’a ba.

Tinubu ya kuma yi gargadi a kan yadda yankin Yammacin Afirka ke fama da rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, ya na mai cewa ta’addanci da rashin tsaro su na matukar kawo koma-baya ga ci-gaban yankin.

Taron ECOWAS karo na 63 dai shi ne na farko da Shugaba Tinubu ya halarta tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya.

Leave a Reply