An ceto leburori 25 da su ka makale a cikin baraguzai, bayan
wani bene mai hawa bakwai da su ke aikin ginawa ya rushe da
su a Jihar Legas.
Gwamnatin Jihar Legas ta sanar da hakan, bayan faruwar iftila’in a ginin da ya rushe yayin da ake tsaka da aikin ginin sa a yankin Banana Island.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar Gbenga Omotoshi ya sanar da haka, inda ya ce mutane 16 da su ka samu raunuka sosai an kwantar da su a asibitoci, ragowar 9 da su ka samu kananan raunuka kuma an riga an sallame su.
Wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ta ce ana ci-gaba da aikin ceto, kuma gwamnatin jihar ta fara gudanar da bincike a kan rushewar da benen mai hawa bakwai ya yi a ranar Larabar da ta gabata.
Kwamishinan ya kara da cewa, Gwamna Babajide jihar ya kuma bada umarnin dakatar da duk aikin gine-ginen da ake yi a yankin domin tantance ingancin su.