Home Labaru Da Dumi-Dumi: Apc Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu Koko

Da Dumi-Dumi: Apc Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu Koko

124
0

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a jihar Kebbi, ya
amince da dakatar da dan majalisar wakilai mai wakiltar
mazabar Koko-Besse da Maiyama Shehu Muhammad Koko
daga halartar ayyukan jam’iyyar.

Dakatarwar dai, ta biyo bayan jerin korafe-korafen da kwamitin ya samu daga karamar hukumar dan majalisar, a kan zarge-zargen ayyukan kin jinin jam’iyyar da ya aikata, wanda zai iya bata masu rai ko kuma ya haifar da matsalar da ka iya janyo rashin tasirin jam’iyyar.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin takardar dakatarwar, wadda shugaban jam’iyyar na jihar Abubakar Muhammad Kana ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.

Kwamitin ayyuka na jihar dai ya amince da dakatar da dan majalisa Shehu Muhammad Koko daga shiga duk wata harka ta APC har sai an kammala binciken korafe-korafen, sannan an gargade shi ya daina bayyana kan sa a matsayin dan jam’iyyar APC.

Leave a Reply