Home Labaru Hakimai Sun Yi Watsi Da Umarnin Gwamna Ganduje

Hakimai Sun Yi Watsi Da Umarnin Gwamna Ganduje

830
0
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Wasu hakimai 11 da su ka fada karkashin sabbin masarautun da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira, sun halarci hawan Sallah a yammacin ranar Litinin da ta gabata, a masarautar sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II.

Hakiman dai, sun halarci hawan na Daushe ne, sabanin umarnin da gwamnatin jihar Kano ta fitar cewa kowane hakimi ya halarci hawan Sallah a karkashin sabon sarkin masarautar sa.

Karanta Labaru Masu Alaka: Shugaban PDP Bai Samu Ikon Bada Shaida A Kotu Ba

Wadanda su ka kaurace wa umarnin Ganduje dai sun hada da hakimin Dawakin Tofa, da na karamar hukumar Doguwa, da hakimin Garko, da hakimin Wudil, da hakimin karamar hukumar Garun Malam, da kuma hakimin karamar hukumar Bichi.

Sauran sun hada da hakimin karamar hukumar Danbatta, da hakimin karamar hukumar Takai, da hakimin warawa, da hakimin karamar hukumar Kiru da kuma hakimin karamar hukumar Gabasawa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ganduje Abba Anwar ya fitar, gwamnatin Kano ta bukaci Hakiman su yi watsi da umarnin sarkin Kano zuwa birnin Kano domin gudanar da hawan sallah.

Leave a Reply