Wani dan majalisar wakilai daga Jihar Imo Ikeanga
Ugochinyere, ya ce wasu daga cikin gwamnonin yankin kudu
maso gabas su na amfana da tashe-tashen hankulan da ake
samu a yankin, shi ya sa suka kasa daukar matakan da su ka
dace domin shawo kan kashe-kashen da ke faruwa.
Ugochinyere, ya ce Nijeriya ta na da karfin da za ta iya amfani da shi ta fuskar tsaro domin kawo karshen matsalolin da su ka addabi yankin, amma dole sai shugabannin da su ka fito daga yankin sun zauna domin daukar matsayin bai-daya, wanda za a yi amfani da shi domin magance matsalar.
Ya ce abin da su ke bukata shi ne samun dawwamammen zaman lafiya a ya nkin kudu maso gabas, saboda yadda yankin ya tabarbare, ganin kashe-kashen da ake samu da lalacewar muhalli da rushewar kayan more rayuwa.
Dan majalisar ya kara da cewa, duk wani shugaban da ke bukatar c-gaba da kuma hadin kan Nijeriya, dole ya bude kofar sa domin ba masu ruwa da tsaki damar gabatar da shawarwari a kan yadda za a kawo karshen matsalar.














































