Home Labaru Amurka: Trump Ya Fasa Kai Hari Iran

Amurka: Trump Ya Fasa Kai Hari Iran

787
0

Rahotanni daga Amirka sun nunar da cewa Shugaba Donald Trump ya bayar da umurnin kai hari kan kasar Iran, sai dai ya janye kudirin nasa sa’o’i kalilan gabanin kaddamaar da hare-haren.

Rahotannin sun nunar da ceawa tuni jiragen sama da na ruwa mallakar Amirkan suka shirya tsab domin fara kaddamar da harin kafi ba su umurnin dakatarwa. Kasashen Amirka da Iran din sun fitar da bayanai mabambanta dangane da yankin da Iran ta kakkabo jirgin sama marar matukin nan mallakar kasar Amirkan, wanda shi ne ya tunzura Trump ya bayar da umurnin kaddamar da yaki kan Iran.

Dakarun juyin-juya halin Musulunci na Iran ne dai suka kakkabo jirgin kana mahukuntan Tehran din suka fitar da hotunan da ke nunar da cewa jirgin na shawagi ne a sararain samaniyar Iran, yayin da sojojin Amirka suka sanar da cewa jirgin yana sararin samaniyar kasa da kasa ne ba na kasar Iran ba.

Tun da fari dai shugaban Amirka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa da ke cewa yana tsammanin Iran ta kakkabo jirfgin ne bisa hadari kafin daga bisani ya bayar da umurnin kai harin da ya dakatar daga baya sakamakon wani taron sirri da ya gudanar da masu ruwa da tsaki kan tsaron kasar.

A nasa bangaren mataimakin shugaban kasar ta Iran din Abbas Araghchi  ya nunar da cewa za su mika kokensu ga Majalisar Dinkin Duniya kan abin da ta kira takalar fada da Amirka ke mata.