Home Labaru Mauritania: An Soma Kada Kuri’a A Zaben Shugaban Kasa

Mauritania: An Soma Kada Kuri’a A Zaben Shugaban Kasa

347
0

A yau asabar mutanen Mauritania ke kada kuria’a dangane da zaben shugaban kasar, mutumen da ake sa ran zai taimaka tare ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma samarwa yan kasar da kayayyakin more rayuwa.

Zaben na yau ya kasance na farko da aka taba samu a karkashin turbar Dimokuradiyya a wanan kasa da ta yi kaurin suna a juyin mulki, daga shekara ta 1978 zuwa 2008.

Yan takara biyar za su fafata da junan su don maye gurbin Shugaban kasar mai barin gado Mohamed Ould Abdel Aziz .

A na dai kalon Shugaban kasar mai barin gado Ould Abdel Aziz a matsayin mutumen da ya taka gaggarumar rawa domin tabbatar da tsaro a wannan kasa mai yawan jama’a da kusan milyan 4 da dubu dari biyar.