Home Labaru Yaki Da Rashawa: Shugaba Buhari Ya Sa Sannu A Wata Dokar Yaki...

Yaki Da Rashawa: Shugaba Buhari Ya Sa Sannu A Wata Dokar Yaki Da Sace Kudin Kasa

405
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannu a kan kudirin dokar taimakon juna na kasa da kasa, ta fuskar samar da bayanan sirri a kan manyan laifuffuka da su ka hada da cin hancin da rashawa.

Kudirin dai ya kunshi samun hadin kai, ko kuma taimakon juna tsakanin kasashe a kan yaki da manyan laifuffuka, ta yadda kasashe za su rika taimaka wa junan su wajen samar da bayanai a kan duk wadanda ke aikata miyagun laifuffuka.

Dokar, za ta tabbatar da nemo inda masu laifin su ke, tare da nuna inda su ka yi ajiyar kudaden su da kaddaorrin da su ka mallaka.

Kasashen, za su taimaka wajen dakile amfani da irin wadannan dukiyoyi da aka same su ta hanyar cin hanci da rashawa ko kuma zamba, sannan a rike dukiyoyin a kuma hana wadanda su ka saci kudin amfani da su, a kuma tabbatar da an maida wa kasar da ke da kudaden kudiyar ta.

Haka kuma, za a tabbatar da an bada bayanan sirri a kan duk wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa domin a gurfanar da su.

Leave a Reply