Home Labaru Kiwon Lafiya Almundahana: Tsohon Minista Ya Karkatar Da Kudin Kiwon Lafiya

Almundahana: Tsohon Minista Ya Karkatar Da Kudin Kiwon Lafiya

325
0
Oly Llung, Tsohon Ministan Lafiya Na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
Oly Llung, Tsohon Ministan Lafiya Na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, jami’an tsaro sun damke tsohon ministan lafiya na kasar Oly Llunga, akan tuhumar da ake masa cewa ya aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Ministan ne ya jagoranci shirin yaki da annobar cutar Ebola na kasar na tsawon fiye da shekara guda.

Tsohon ministan ya yi farin jini a shekarun baya, amma yanzu ana tuhumarsa da karkatar da kudaden da aka ware domin yakar annobar Ebola.

Jami’an ‘yan sandan Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun fara gudanar da bincike kan batun kuma Oly Llunga ya sha tambayoyi a hannun su, sai dai ya musanta aikata wani laifi kan wannan batun.

Mista Lunga wanda ya ajiye aikinsa na minista ne a watan Yulin da ya gabata, jim kadan bayan an tube shi daga mukamin.

Fiye da mutum 2000 sun rasa rayukansu tun da cutar ta bayyana a yankunan gabashin kasar na Ituri da Arewacin Kivu.