Home Labaru Matakan Tsaro: Za A Ci Gaba Da Rufe Iyakkokin Nijeriya Har Sai...

Matakan Tsaro: Za A Ci Gaba Da Rufe Iyakkokin Nijeriya Har Sai An Cimma Manufa – Monguno

517
0
Manjo Janar Babagana Monguno, Babban Mai Ba Kasa Shawara Ta Fuskar Tsaro
Manjo Janar Babagana Monguno, Babban Mai Ba Kasa Shawara Ta Fuskar Tsaro

Babban mai ba kasa shawara ta fuskar tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya ce iyakokin Nijeriya za su cigaba da kasancewa rufe har sai an cimma manufofin da ke tattare da kulle su.

Monguno ya bayyana wa manema laarai cewa, aikin hadin gwiwa na tsaro da ke gudana, wanda ya sa aka rufe iyakokin zai fi kwanaki 28 da aka bayyana da farko, sannan zai cigaba da kasancewa a haka har sai an cimma manufofin.

Ya ce babu rana ko wa’adin da za su kammala shirin, sannan sun fara ganin sakamako mai kyau, ya na mai cewa, shirin ya na daga cikin kokarin raba Nijeriya da miyagun ayyuka, ciki har da fasa-kwauri da kuma habbaka tattalin arziki.

Monguno ya kara da cewa, lamarin rashin tsaro ya na kara tabarbarewa sakamakon damar da masu fasa-kwauri ke samu ta iyakokin Nijeriya, don haka ya bukaci hadin kai daga kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya domin cimma manufar shirin.