Shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sha ihu a yayin da ya shirya yin jawabi a jana’izar tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe a birnin Harare.
Ba shiri dai Shugaba Cyril Ramaphosa ya sauya jawabin girmama marigayin ya zuwa na neman afuwar jama’a da suka ki yin shiru har sai da ya nemi gafara kan rikicin kin jinin baki da ya salwantar da rayuka da kuma dukiya a kasar sa ta Afirka ta Kudu.
Ramaphosa ya sha suka kan yadda ya gagara shawo kan rikicin na kin jinin duk wanda ba dan kasar ba, inda daga bisani an shawo kan jama’a aka ci gaba da gudanar da taron bankwana kamar yadda aka tsara tun daga farko.
Robert Mugabe, ya mutu ne a makon da ya gabata ya na
da shekaru 95 bayan fama da jinya a wani asibiti da ke a kasar Singapore.
You must log in to post a comment.