Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da hukuncin
ɗaurin shekaru takwas da aka yanke wa tsohon Shugaban
Kwamitin Kula da Fansho Abdulrasheed Maina bisa yin
sama-da-faɗi da kuɗaɗen fansho Naira biliyan 2 da miliyan
100.
Alƙala uku da su ka saurari shari’ar baki ɗaya sun yi ittifaƙi a kan tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina kamar yadda Mai Shari’a Okon Abang ya karanto.
Jagoran alƙalan mai shari Elfreda Williams-Daudu, ya tabbatar da hukuncin da Babbar Kotu ta yanke wa Maina, wanda a kan haka ne ya ɗaukaka ƙara.
Alƙalin ya ce an yi wa Maina adalci wajen sauraren shari’ar, domin mai tuhuma ya gabatar da hujjoji gamsassu.














































