Home Labarai Za Mu Ci Gaba Da Tuna ‘Yar’Adua Saboda Cigaban Da Ya Kawo...

Za Mu Ci Gaba Da Tuna ‘Yar’Adua Saboda Cigaban Da Ya Kawo Wa Nijeriya – Jonathan

107
0

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana
tsohon maigidan sa marigayi Umaru ‘Yar’adua a matsayin
shugaba maras son zuciya.

Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne, a wani ɓangare na ranar cika shekaru 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Jonathan Nijeriya ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya wato marigayi Umaru Musa Yar’Adua, domin mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya,

Ya ce Shugaba Yar’Adua jagora ne abin misali, wanda ya rayu ba tare da nuna bambancin ƙabilanci ko na addini ba, kuma gudunmawar sa a fagen aikin gwamnati ta zaburar da mutane da yawa a kan hanyar alheri.

Goodluck Jonathan, ya ce za a cigaba da tunawa da ‘Yar’adua saboda gagarumin ci-gaban da ya kawo da kuma himmar sa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci-gaban Nijeriya.

Leave a Reply